Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 17:11 - Sabon Rai Don Kowa 2020

11 sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

11 Sa'ad da lokacinka ya yi da za ka mutu, zan ta da ɗaya daga cikin zuriyarka, ɗaya daga cikin 'ya'yanka maza, zan kafa mulkinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 17:11
21 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,


“Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe.


“’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau.


Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki.


Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya.


Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila.


“Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina, yanzu kuma ga shi na zauna a kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya yi alkawari, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.


Sa’an nan Dawuda ya huta tare da kakanninsa. Sai aka binne shi a Birnin Dawuda.


In ba haka, bayan an binne ranka yă daɗe sarki, tare da kakanninsa, za a wulaƙance ni da Solomon ɗana, kamar masu laifi.”


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Za ka huta tare da kakanninka, waɗannan mutane kuwa ba da daɗewa ba za su yi karuwanci ga baƙin alloli na ƙasar da za su shiga. Za su yashe ni su kuma karya alkawarin da na yi da su.


Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa.


Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikali, amma ɗanka, wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’


da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “ ‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida,


Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.


Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra’ila ba,


Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’


Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ