1 Tarihi 15:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki16 Dawuda ya umarci shugabannin Lawiyawa su sa 'yan'uwansu mawaƙa su riƙa raira waƙa da murna, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, da molaye, da garayu, da kuge masu amon gaske. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera, “Yana da kyau; ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije,
sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.
Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.