Zai zama kamar sa’ad da mai girbi ya tara hatsin da yake tsaye ya kuma girbe hatsin da hannunsa kamar sa’ad da mutum ya yi kala kawunan hatsi a Kwarin Refayim.
A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.
Sa’ad da Filistiyawa suka ji an naɗa Dawuda sarki a bisa dukan Isra’ila, sai suka haura da cikakken mayaƙa don su neme shi, amma Dawuda ya ji game da wannan ya kuwa fita don yă ƙara da su.