6 Elkana, Isshiya, Azarel, Yoyezer da Yashobeyam daga Kora;
’Ya’yan Kora maza, su ne, Assir, Elkana da Abiyasaf. Waɗannan su ne dangin Kora.
Ɗan Uzzi shi ne, Izrahiya. ’Ya’yan Izrahiya maza su ne, Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne.
Eluzai, Yerimot, Beyaliya, Shemariya da Shefatiya daga Haruf;
da Yoyela da Zebadiya ’ya’yan Yeroham maza daga Gedor.