Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tarihi 12:23 - Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Ga yawan mutanen shiryayyu don yaƙi waɗanda suka zo wurin Dawuda a Hebron don su mai da mulkin Shawulu gare shi, yadda Ubangiji ya faɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

23 Horarrun sojoji da yawa suka haɗa kai da sojojin Dawuda a Hebron domin su taimaki Dawuda da yaƙi, su mai da shi sarki maimakon Saul, kamar yadda Ubangiji ya alkawarta. Ga yadda yawansu yake.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tarihi 12:23
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan su ne manyan jarumawan Dawuda, su ne, tare da dukan Isra’ila, suka ba wa mulkinsa goyon baya mai ƙarfi da ya kai bisa dukan ƙasar, yadda Ubangiji ya yi alkawari.


Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Har yaushe za ka yi ta makoki saboda Shawulu? Na riga na ƙi shi da zaman sarkin Isra’ila. Ka cika ƙahonka da mai, zan aike ka zuwa wurin Yesse na Betlehem. Na zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza yă zama sarki.”


Ka gayyato Yesse a wurin hadayar, ni kuma zan gaya maka abin da za ka yi. Za ka shafe mini wanda na nuna maka.”


“Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”


bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.


To, yanzu sai ku yi haka! Gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta wurin bawana Dawuda zan ceci mutanena Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da kuma hannun dukan abokan gābansu.’ ”


Mutanen Yahuda, masu riƙe garkuwa da māshi, su 6,800 shiryayyu don yaƙi;


Sai Yaƙub ya aiki manzanni su sha gabansa zuwa wurin ɗan’uwansa Isuwa a ƙasar Seyir, a ƙauyen Edom.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ