1 Tarihi 11:10 - Sabon Rai Don Kowa 202010 Waɗannan su ne manyan jarumawan Dawuda, su ne, tare da dukan Isra’ila, suka ba wa mulkinsa goyon baya mai ƙarfi da ya kai bisa dukan ƙasar, yadda Ubangiji ya yi alkawari. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki10 Waɗannan su ne shugabanni, wato manyan jarumawan Dawuda waɗanda suka goyi bayansa sosai a mulkinsa, tare da dukan Isra'ilawa waɗanda suka naɗa shi sarki bisa ga maganar Ubangiji a kan Isra'ilawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.