45 Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.
Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi.
’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefo, Gatam da Kenaz.
Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.
Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.
Jarumawanki, ya Teman, za su razana, za a kashe kowane mutum a duwatsun Isuwa.