Ubangiji ya yi daidai yadda ya yi wa zuriyar Isuwa waɗanda suka zauna a ƙasar Seyir, sa’ad da ya hallaka Horiyawa a gabansu. Su kuma suka kore su, suka zauna a wurinsu. Har wa yau, zuriyar Isuwa ne suke zama a can.
Haka ma Horiyawa, a dā sun zauna a Seyir, amma zuriya Isuwa suka kore su. Suka hallaka Horiyawa da suke kafinsu, suka kuma zauna a wurinsu, kamar dai yadda Isra’ila ta yi a ƙasar da Ubangiji ya ba su a matsayin mallaka.)