21 wato, waɗanda suka ragu a ƙasar, waɗanda Isra’ilawa ba su iya hallakawa ba, su ne Solomon ya ɗauka su zama bayinsa don aikin gandu, kamar yadda yake har wa yau.
Ko da yake mutanen Benyamin sun kāsa su kori Yebusiyawa, waɗanda suke zaune a Urushalima; har yă zuwa yau, Yebusiyawa suna zaune a can tare da mutanen Benyamin.
Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam,
Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer.
Dawuda kuwa ya umarta a tattara baƙin da suke zama a Isra’ila, daga cikinsu ya sa masu farfasa duwatsu don su shirya duwatsun da aka sassaƙa saboda ginin gidan Allah.
wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau.
Ba su kori Kan’aniyawan da suke zama a Gezer ba, don haka Kan’aniyawa suna zama tare da mutanen Efraim har wa yau; amma Kan’aniyawa suka zama masu yin aikin dole.