Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila.
Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.