Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 7:23 - Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Sai Huram ya yi wani ƙaton kwano na ƙarfen tagulla, da ya kira Teku. Zurfin kwanon nan kamu bakwai da rabi, fāɗinsa kamu goma sha biyar, da’irarsa kuma kamu talatin ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

23 Huram kuma ya yi kewayayyiyar babbar kwatarniya ta zubi da tagulla. Faɗinta kamu goma ne, tsayinta kuwa kamu biyar, da'irarta kuma kamu talatin ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 7:23
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya yi ƙaton kwano mai suna Teku na zubin ƙarfe, mai siffar da’ira, awonsa kamu goma ne daga da’ira zuwa da’ira tsayinsa kuma kamu biyar. Ya ɗauki magwaji mai tsawo kamu talatin ya auna shi kewaye.


Babiloniyawan kuma suka sassare ginshiƙan tagulla, da wuraren zama da za a iya matsar da su, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla da yake a haikalin Ubangiji, suka kwashe tagullan zuwa Babilon.


Babiloniyawa kuwa suka farfasa ginshiƙan tagulla, da dakalai, da babbar kwatarniya, waɗanda suke a haikalin Ubangiji. Suka kwashe tagulla duka suka kai Babilon.


Tagullar da sarki Solomon ya yi wa haikalin Ubangiji da ita, wato, ginshiƙai biyu, da ƙaton kwano mai suna Teku na tagulla, da bijimai goma sha biyu, waɗanda suke ɗauke da kwatarniya, da dakalai, ta fi ƙarfin a auna.


Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam.


Suka yi daro da gammonsa da tagulla daga madubai na mata masu yin aiki a ƙofar Tentin Sujada.


Sarkin Ahaz ya kawar da katakon ya kuma ɗauke tasoshin daga mazauninsu da ake iya matsarwa. Ya ɗauke ƙaton kwano mai suna Teku daga kan bijiman tagullar da ya tallafe su ya ajiye a kan mazaunin dutse.


Dajiyoyin da suke a bisa suna da fasalin bi-rana ne. Ta haka aka gama aiki a kan ginshiƙan.


ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa;


Sarkin Ahaz ya umarci Uriya cewa, “A kan babban sabon bagade, ka miƙa hadayar ƙonawa ta safe, da hadayar hatsi ta yamma, da hadayar sarki ta ƙonawa da hadayarsa ta hatsi, da hadaya ta dukan jama’ar ƙasar, tare da hadayan hatsinsu da kuma ta sha. Ka yayyafa jinin hadayun ƙonawa a kan bagade. Amma zan yi amfani da bagaden tagulla don neman bishewa.”


Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da ginshiƙai, kwatarniya, da dakalai, da sauran kayayyaki da aka bar su a birnin nan,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ