1 Sarakuna 7:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 wanda mahaifiyarsa gwauruwa ce daga kabilar Naftali, wanda kuma mahaifinsa mutumin Taya ne, shi Huram, gwani ne a aikin tagulla. Huram gwani ne sosai kuma ya saba da yin kowane irin aikin tagulla. Sai ya zo wurin Sarki Solomon ya kuma yi dukan aikin da aka sa shi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Shi ɗan wata mata ne daga kabilar Naftali wadda mijinta ya rasu. Huram mutumin Taya ne, maƙerin tagulla. Yana da hikima, da fahimi, da fasaha na iya yin kowane irin aiki da tagulla. Ya kuwa amsa kiran sarki Sulemanu, ya zo ya yi masa dukan aikinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
wanda mahaifiyarsa ta fito daga Dan, mahaifinsa kuma daga Taya. An horar da shi a aikin zinariya, azurfa, tagulla, baƙin ƙarfe, dutse, itace, da kuma shuɗi, shunayya, garura, da lilin mai kyau. Ya gogu a kowane irin zāne-zāne, zai kuma iya yin kowane zānen da aka ba shi. Zai yi aiki tare da masu sana’arka, da kuma tare da waɗanda ranka yă daɗe, Dawuda mahaifinka ya tanada.