Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 6:16 - Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi a can ƙuryar haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

16 Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi can ƙuryar Haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al'ul tun daga ƙasa har sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 6:16
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya gina Wuri Mafi Tsarki, tsawonsa daidai da fāɗin haikalin. Tsawonsa kamu ashirin, fāɗinsa kuwa kamu ashirin. Ya shafe cikin da talenti ɗari shida na zinariya zalla.


Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji inda aka shirya masa, can ciki cikin haikali, a Wuri Mafi Tsarki, aka kuma sa shi a ƙarƙashin fikafikan kerubobin.


Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,


Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa ɗan’uwanka Haruna, kada yă riƙa shiga Wuri Mafi Tsarki bayan labule koyaushe, wato, a gaban murfi wanda yake bisa akwatin alkawari, domin kada yă mutu, gama zan bayyana a cikin girgije a kan murfin.


A cikin yanki mai tsarki, ka auna tsawo kamu 25,000 da kuma fāɗi kamu 10,000. A cikinsa wuri mai tsarki zai kasance, Wuri Mafi Tsarki.


A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe.


ka kuma kafa katakai biyu a kusurwoyi can ƙarshe.


Tsawon babban zaure a gaban wannan ɗaki, kamu arba’in ne.


Ya kuma gina shirayi ta sarauta, da ya kira Zauren Adalci, inda zai riƙa yin shari’a, ya kuma rufe dukan daɓensa da itacen al’ul daga ƙasa har sama.


Ya kuma auna tsawon wuri mai tsarki da yake can ciki; tsawon kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu ashirin daga ƙurewa wuri mai tsarki da yake waje. Ya ce mini, “Wannan shi ne Wuri Mafi Tsarki.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ