A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.
Sa’ad da aka gama aikin da Sarki Solomon sa a yi domin haikalin Ubangiji, sai ya kawo kayayyakin da mahaifinsa Dawuda ya keɓe, azurfa da zinariya da kayayyaki, ya sa su a ma’ajin haikalin Ubangiji.
Sau uku a shekara Solomon kan miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama a kan bagaden da ya gina wa Ubangiji, yana ƙone turare a gaban Ubangiji haɗe da su, ta haka ya cika abin da ake bukata na haikali.