Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 4:24 - Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

24 Sulemanu ya mallaki dukan ƙasar da yake yamma da Kogin Yufiretis, daga Tifsa har zuwa birnin Gaza. Ya mallaki dukan sarakuna yammacin Yufiretis. Akwai zaman lafiya ko'ina a mulkinsa da ƙasashen maƙwabta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 4:24
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma za ka haifi ɗa wanda zai zama mutumin salama da kuma hutu, zan kuma ba shi hutu daga dukan abokan gābansa a kowane gefe. Za a kira shi Solomon, zai kuma kawo wa Isra’ila salama da natsuwa a zamanin mulkinsa.


Dukan sarakuna za su rusuna masa kuma dukan al’ummai za su bauta masa.


har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.


“Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”


Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


Duwatsu za su kawo wadata ga mutane, tuddai kuma su ba da amfani na adalci.


Amma yanzu Ubangiji Allahna ya ba ni hutu a kowane gefe, babu kuma gāba ko masifa.


Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa.


Wata rana Samson ya tafi Gaza, inda ya ga wata karuwa. Ya shiga wurinta ya kwana.


Mutanen Yahuda kuma suka ci Gaza, Ashkelon, da Ekron, kowace birni tare da yankinsa.


shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.


Ya yi mulki bisa dukan sarakuna daga Kogi Yuferites zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar.


Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ