Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi.
“Ka lura da yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana kuwa? Domin ya ƙasƙantar da kansa, ba zan kawo wannan masifa a kwanakinsa ba, amma zan kawo ta a kan gidansa a kwanakin ɗansa.”