1 Sarakuna 2:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 domin Ubangiji ya cika maganar da ya faɗa mini cewa, ‘Idan 'ya'yanka suna lura da hanyarsu, sun yi tafiya a gabana da gaskiya da zuciya ɗaya, da dukan ransu, ba za ka rasa mutum wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Yanzu, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari ka cika wa bawanka Dawuda mahaifina alkawaran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza sun yi hankali cikin dukan abubuwan da suke yi, don su yi tafiya a gabana kamar yadda ka yi.’
Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.
“Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’