Sai ya ci gaba, “In kin yarda, ki yi magana da Sarki Solomon, gama ba zai ƙi jinki ba, ki ce yă ba ni yarinyan nan, Abishag, mutuniyar Shunam, tă zama matata.”
Sai Batsheba ta tafi wurin Sarki Solomon don tă yi masa magana a kan Adoniya. Sarki ya miƙe tsaye don yă sadu da ita, ya rusuna mata, ya kuma zauna a kujerar sarautarsa. Ya sa aka kawo wa mahaifiyar sarki kujerar sarauta, ta kuwa zauna a gefen damansa.