Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.
Yayinda yake a Masar, Hadad ya ji Dawuda ya huta tare da kakanninsa, ya kuma ji cewa Yowab shugaban mayaƙa ya mutu. Sai Hadad ya ce wa Fir’auna, “Bari in tafi, don in koma ƙasata.”
Sai Sarki Solomon ya tattara dattawan Urushalima a gabansa, da dukan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalan Isra’ilawa, domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.
Sai Rehobowam ya huta da kakanninsa, aka kuma binne shi tare da su a Birnin Dawuda. Sunan mahaifiyarsa Na’ama, ita kuwa mutuniyar Ammon ce. Sai Abiyam ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
Ahaziya ɗan Ahab ya zama sarkin Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekaru biyu.