1 Sarakuna 18:36 - Sabon Rai Don Kowa 202036 A lokacin hadaya, sai annabi Iliya ya zo gaba ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Ibrahim, na Isra’ila da kuma na Yaƙub, bari a sani a yau cewa kai Allah ne a cikin Isra’ila, a kuma san cewa ni bawanka ne, na kuma yi dukan waɗannan abubuwa bisa umarninka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki36 A lokacin miƙa hadaya ta maraice, sai annabi Iliya ya matso kuwa, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Ibrahim, da Ishaku, da Isra'ila, bari ya zama sananne a wannan rana, cewa kai ne Allah a Isra'ila, ni kuma bawanka ne, na yi waɗannan abubuwa duka bisa ga maganarka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan aika suka tafi ko’ina a Isra’ila da Yahuda da wasiƙu daga sarki da kuma daga fadawansa, wasiƙar tana cewa, “Mutanen Isra’ila, ku dawo ga Ubangiji Allah na Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, domin yă dawo gare ku, ku da kuka tafi, ku da kuka kuɓuce daga hannun sarakuna Assuriya.