1 Sarakuna 18:26 - Sabon Rai Don Kowa 202026 Sai suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi. Sa’an nan suka kira bisa sunan Ba’al daga safe har tsakar rana. Suna ihu, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma babu wata amsa, babu wani da ya amsa. Suka yi ta rawa kewaye da bagaden da suka yi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki26 Suka kuwa kama bijimin da aka ba su, suka gyara shi suka yi ta kira ga sunan Ba'al tun da safe, har tsakar ranar suna ta cewa, “Ya Ba'al, ka amsa mana!” Amma ba murya, ba kuwa wanda ya amsa. Suka yi ta tsalle a wajen bagaden da suka gina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.