Sa’an nan ya aika saƙo ko’ina a Isra’ila, dukan masu yi wa Ba’al hidima kuwa suka tattaru, ba mutumin da bai zo ba. Suka yi cincirindo a haikalin Ba’al har sai da ya cika makil.
Yoram ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar yadda mahaifinsa da mahaifiyarsa suka yi ba. Ya kawar da dutsen tsarkin Ba’al wanda mahaifinsa ya yi.
Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al.