1 Sarakuna 16:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 “Na ɗaga ka daga ƙura na mai da kai shugaban mutanena Isra’ila, amma ka yi tafiya a hanyoyin Yerobowam, ka kuma sa mutanena Isra’ila suka yi zunubi, ka tsokane ni na yi fushi ta wurin zunubansu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 “Tun da yake na ɗauke ka daga cikin ƙura, na maishe ka shugaban jama'ata Isra'ila, kai kuwa ka bi hanyar Yerobowam, ka sa jama'ata, wato Isra'ila, su yi zunubi, suka sa na yi fushi saboda zunubansu, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’