21 Da Ba’asha ya ji haka, sai ya daina ginin Rama, ya janye zuwa Tirza.
21 Da Ba'asha ya ji labari, sai ya daina ginin Rama, ya tafi ya zauna a Tirza.
Sai matar Yerobowam ta tashi ta tafi, ta kuwa tafi Tirza. Nan da nan da ta taka madogarar ƙofar gidan, sai yaron ya mutu.
Ke kyakkyawa ce, ƙaunatacciyata, kamar Tirza, kyakkyawa kuma kamar Urushalima, mai daraja kamar mayaƙa da tutoti.
Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.
Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura, ya yi yaƙi da Yahuda, ya kuma gina Rama don yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa, sarkin Yahuda.
Ba’asha ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Tirza. Sai Ela ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.
A shekara ta talatin da ɗaya na Asa sarkin Yahuda, Omri ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu, shekaru shida a Tirza.