Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Sarakuna 15:19 - Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakanina da kai, kamar yadda ta kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Duba, ina aika maka kyautai na azurfa da na zinariya. Yanzu fa sai ka janye yarjejjeniyarka da Ba’asha sarkin Isra’ila, don yă janye daga gare ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

19 “Bari mu ƙulla alkawari da juna kamar yadda tsohona da tsohonka suka yi, ga shi, na aika maka da kyautar azurfa da zinariya. Sai ka tafi, ka warware alkawarinka da Ba'asha, Sarkin Isra'ila, domin ya tashi ya bar ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Sarakuna 15:19
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

In haka ne, “Ba sai mu yi ta yin mugunta don yă zama hanyar samun nagarta ba”? Kamar yadda masu baƙar magana game da mu suna cewa wai haka muke faɗa. Tabbatacce za a hukunta irin waɗannan da hukuncin da ya dace da su.


su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi.


Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.


Yehu mai duba, ɗan Hanani, ya fita don yă tarye shi, ya kuma ce wa sarki, “Ya yi kyau ke nan da ka taimaki mugu ka kuma ƙaunaci waɗanda suke ƙin Ubangiji? Da yake ka yi haka fushin Ubangiji yana a kanka


A lokacin Hanani mai duba ya zo wurin Asa sarkin Yahuda ya ce masa, “Don ka dogara ga sarkin Aram, ba kuwa ga Ubangiji Allahnka ba ne mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka.


Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.”


Sai sarki ya tattara Gibeyonawa ya yi musu magana. (To, Gibeyonawa ba sashen Isra’ilawa ba ne, amma mutanen Amoriyawa ne da suka ragu, waɗanda Isra’ila ta rantse za tă bari da rai, amma Shawulu cikin kishinsa don Isra’ila da Yahuda ya yi ƙoƙari yă hallaka su duka.)


Aka yi yaƙi tsakanin Asa da Ba’asha sarkin Isra’ila dukan kwanakin mulkinsu.


Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ