1 Sarakuna 14:23 - Sabon Rai Don Kowa 202023 Sun kuma kafa wa kansu masujadai da suke kan tuddai, da a kan keɓaɓɓun duwatsu, suka kuma gina ginshiƙan Ashera a kowane tudu, da kuma a ƙarƙashin kowane duhuwar itace. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki23 Gama su ma sun gina wa kansu wuraren tsafi a tuddai, da ginshiƙai, da gumaka a tuddai, da cikin duhuwar itatuwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za su kuwa san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da gawawwakin mutanensu suna kwance a kusa da gumakansu da kewaye da bagadansu, a kowane kan tudu mai tsawo da kuma a kan dukan kan duwatsu, a ƙarƙashin kowane inuwar itace da kuma kowane oak mai ganye, wuraren da suke ƙone turare masu ƙanshi wa dukan gumakansu.