1 Sarakuna 11:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka.
Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.