1 Sarakuna 11:34 - Sabon Rai Don Kowa 202034 “ ‘Amma ba zan ɗauki dukan masarautar daga hannun Solomon ba; na naɗa shi sarki, dukan kwanaki ransa saboda Dawuda bawana, wanda na zaɓa, wanda kuma ya kiyaye umarnai da farillaina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki34 Duk da haka ba zan karɓe sarauta duka daga hannunsa ba, amma zan bar shi ya yi mulki muddin ransa saboda bawana Dawuda, wanda na zaɓa, wanda ya kiyaye umarnaina da dokokina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Zan yi wannan domin sun yashe ni, suka kuma yi wa Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Kemosh, allahn Mowabawa, da kuma Molek, allahn Ammonawa sujada, ba su yi tafiya a hanyoyina ba, ba su kuwa yi abin da yake daidai a idanuna ba, ba su kiyaye farillaina da dokokina kamar yadda Dawuda, mahaifin Solomon ya yi ba.