1 Samaʼila 6:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 Lawiyawa suka saukar da akwatin alkawarin Ubangiji tare da babban akwati mai siffofin zinariya na ɓeraye da marurai suka ajiye su a kan ƙaton dutse. A wannan rana mutanen Bet-Shemesh suka miƙa hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu ga Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki15 Lawiyawa kuwa suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji da akwatin da yake gefensa wanda aka sa siffofin zinariya a ciki. Suka ajiye su a kan babban dutsen. Mutanen Bet-shemesh kuwa suka miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu kuma a wannan rana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Filistiyawa kuma suka aika da siffofin ɓeraye biyar na zinariya. Yawan ɓerayen sun yi daidai da yawan garuruwan sarakunan nan biyar na Filistiyawa. Garuruwan sun ƙunshi waɗanda aka gina katangar birni kewaye da su, da kuma ƙauyukansu. Babban dutsen da suka ajiye akwatin alkawarin Ubangiji, ya zama shaida har wa yau a filin Yoshuwa a Bet-Shemesh.