1 Samaʼila 6:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 Keken shanun ya zo filin Yoshuwa a Bet-Shemesh ya tsaya a gefen wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun suka miƙa shanun hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Keken shanun kuwa ya shiga gonar Joshuwa mutumin Bet-shemesh, ya tsaya a wurin, kusa da wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun, suka yanka shanun suka ƙone su hadaya ga Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Filistiyawa kuma suka aika da siffofin ɓeraye biyar na zinariya. Yawan ɓerayen sun yi daidai da yawan garuruwan sarakunan nan biyar na Filistiyawa. Garuruwan sun ƙunshi waɗanda aka gina katangar birni kewaye da su, da kuma ƙauyukansu. Babban dutsen da suka ajiye akwatin alkawarin Ubangiji, ya zama shaida har wa yau a filin Yoshuwa a Bet-Shemesh.