1 Samaʼila 29:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Dawuda ya ce wa Akish, “Me na yi? Ka taɓa samun bawanka da laifi tun daga ranar da na zo har zuwa yanzu? Ina dalilin da ba zan tafi tare da kai in yaƙi maƙiyin ranka yă daɗe, sarki ba?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Dawuda ya ce wa Akish, “Me na yi? Wane laifi ka samu a wurin baranka tun daga ranar da na shiga hidimarka har zuwa yau, da ba zan tafi in yi yaƙi da abokan gāban ubangijina sarki ba?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”