1 Samaʼila 28:15 - Sabon Rai Don Kowa 202015 Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Don me ka dame ni, ta wurin hauro da ni?” Shawulu ya ce, “Ina cikin babban damuwa ce, Filistiyawa sun fāɗa mini, Allah kuma ya juya mini baya. Bai amsa mini, ko ta mafarki, ko kuma ta annabawa ba, saboda haka na kira ka don ka gaya mini abin yi.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki15 Sai Sama'ila ya ce wa Saul, “Don me ka dame ni, ka hawar da ni?” Saul ya ce, “Ina cikin babbar wahala, gama Filistiyawa suna yaƙi da ni, Allah kuma ya rabu da ni, ya ƙi amsa mini ko ta wurin annabawa ko ta mafarkai, saboda haka na kira ka, ka faɗa mini abin da zan yi.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |