1 Samaʼila 25:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Tambayi samarinka, za su faɗa maka. Saboda haka ka yarda samarina su sami tagomashi a wurinka, gama yau ranar biki ce. Muna roƙonka ka ba barorinka, da ɗanka, Dawuda abin da za ka iya ba mu.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
a matsayin lokacin da Yahudawa suka sami huta daga abokan gābansu, da kuma a matsayin watan da aka mai da baƙin cikinsu ya zama farin ciki, makokinsu kuma ya zama ranar biki. Ya rubuta musu su kiyaye ranakun a matsayin ranakun biki da na farin ciki. Su kuma ba da kyautai na abinci ga juna, da kuma kyautai ga matalauta.