Saboda haka sarki bai saurari mutane ba, gama wannan juyin al’amura daga Allah ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi ga Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya mutumin Shilo.
A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina.
Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe. Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar.
Amma ku zuba ido ku ga in ya haura zuwa yankinsa, zuwa Bet-Shemesh, to, Ubangiji ne ya kawo mana babban masifar a kanmu. Amma in bai bi ta nan ba, za mu san cewa ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”
Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi.