1 Samaʼila 25:26 - Sabon Rai Don Kowa 202026 Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki26 Yanzu, ya maigida, na rantse da ran Ubangiji da kuma ranka, ka ga Ubangiji ya hana ka zubar da jini, da ɗaukar wa kanka fansa, sai ka bar maƙiyanka da waɗanda suke nema su cuce ka su zama kamar Nabal. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!