Bayan Dawuda ya ƙidaya mayaƙan, lamirinsa ya kāshe shi, sai ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka ka gafarta wa bawanka. Na yi wauta ƙwarai.”
Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Ubangiji sa’ad da ka ji abin da na faɗa game da wannan wuri da mutanen wurin, cewa za su zama la’antattu da kuma kango, domin kuma ka kece tufafinka, ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.
Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa.
Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”