1 Samaʼila 24:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 Baba, duba, ga shafin rigarka a hannuna. Tun da yake na yanki shafin rigarka ban kuwa kashe ka ba, sai ka sani ba ni da niyyar yi maka mugunta. Ban yi maka laifi ba, ko da yake kana farautar raina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”