1 Samaʼila 2:35 - Sabon Rai Don Kowa 202035 Zan tayar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so yă yi, zan kuwa ba shi zuriya da koyaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki35 Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da ko yaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
In ka aikata dukan abin da na umarce ka, ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi abin da yake daidai a idanuna ta wurin kiyaye farillaina da umarnaina, kamar yadda Dawuda bawana ya yi, zan kasance tare da kai. Zan gina maka masarauta mai dawwama kamar wadda na gina wa Dawuda, zan kuma ba da Isra’ila gare ka.
Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”