27 Dawuda da mutanensa suka fita suka kashe Filistiyawa ɗari biyu, suka kawo loɓar suka miƙa wa sarki, domin yă zama surukin sarki. Sai Shawulu ya ba da ’yarsa Mikal aure ga Dawuda.
Saboda haka Shawulu bai yarda Dawuda yă zauna tare da shi ba, amma ya maishe shi shugaban sojoji dubu. Dawuda kuwa ya riƙa bi da su yana kaiwa yana kuma da tare da su.
Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko masa da iko. Sai ya fita ya gangara zuwa Ashkelon, ya kashe mutanensu talatin, ya kwashe kayansu ya kuma ba da rigunarsu ga waɗanda suka bayyana kacici-kacicin. Cike da fushi, ya haura zuwa gidan mahaifinsa.
Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”
Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”