Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 18:25 - Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Sai Shawulu ya ce, “Ku gaya wa Dawuda, ‘Sarki ba ya bukatan kuɗin auren ’yarsa, sai dai loɓar Filistiyawa domin ramako a kan abokan gābansa.’ ” Shawulu yana shiri ne domin Dawuda yă fāɗa a hannun Filistiyawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

25 Saul kuma ya ce, “Haka za ku faɗa wa Dawuda, ‘Sarki ba ya so ka ba da sadaki don auren, sai dai ka ba da loɓar Filistiyawa guda ɗari, domin ka ɗauki fansa a kan maƙiyan sarki.’ ” (Saul dai yana so Filistiyawa su kashe Dawuda kawai.)

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 18:25
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Shawulu ya ce wa Dawuda, “Ga diyata Merab zan ba ka ka aura, kai dai ka yi mini aiki da himma, ka kuma yi yaƙe-yaƙen Ubangiji.” Saboda Shawulu ya ce wa kansa, “Ba zan ɗaga hannuna a kansa ba, Filistiyawa ne za su yi wannan.”


A wannan rana, Isra’ilawa suka sha wahala ƙwarai domin Shawulu ya sa mutane suka yi rantsuwa cewa, “La’ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin fāɗuwar rana, kafin in ɗauki fansa a kan abokan gābana.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.


Ku faɗa mini nawa ne dukiyar aure da kuma sadakin da zan kawo bisa ga yadda kuke so, zan kuwa biya duk abin da kuka ce. Ku dai bar ni in aure yarinyar ta zama matata.”


Bawanka ya kashe zaki da beyar, wannan Bafilistin marar kaciya zai zama kamar ɗaya daga cikinsu, domin ya rena rundunar Allah mai rai.


Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?”


Sai Yoshuwa ya yi wuƙaƙe na duwatsu, ya yi wa Isra’ilawa kaciya a Gibeyat-Ha’aralot.


Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar ’yarka Rahila.”


Da ma’aikatan Shawulu suka gaya masa abin da Dawuda ya faɗa.


Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”


Shawulu ya gaya wa ɗansa Yonatan da ma’aikatansa su kashe Dawuda. Amma Yonatan yana son Dawuda sosai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ