1 Samaʼila 17:26 - Sabon Rai Don Kowa 202026 Dawuda ya tambayi mutanen da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilistin nan, ya kuma cire wannan kunya daga Isra’ila? Wane ne wannan bafilistin marar kaciya da yake kalubalantar rundunar yaƙi na Allah mai rai?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki26 Sai Dawuda ya tambayi mutanen da suke kusa da shi, ya ce, “Me za a yi wa wanda ya kashe Bafilisten nan, har ya kawar da zargi daga Isra'ila? Gama wane ne wannan Bafiliste, marar kaciya, da zai raina rundunar Allah mai rai?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.