Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 16:1 - Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Har yaushe za ka yi ta makoki saboda Shawulu? Na riga na ƙi shi da zaman sarkin Isra’ila. Ka cika ƙahonka da mai, zan aike ka zuwa wurin Yesse na Betlehem. Na zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza yă zama sarki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

1 Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Har yaushe za ka yi ta ɓacin rai saboda Saul? Ga shi kuwa, na ƙi shi da zama Sarkin Isra'ila. Ka sami man zaitun ka ɗauka. Zan aike ka zuwa wurin Yesse mutumin Baitalami, gama na zaɓi ɗaya daga cikin 'ya'yansa maza ya zama sarki.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 16:1
34 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Elisha ya kira wani daga cikin ƙungiyar annabawa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kwalabar mai ka je Ramot Gileyad.


Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”


Daga wannan rana Sama’ila bai ƙara saduwa da sarki Shawulu ba, har rasuwar Sama’ila, amma ya yi baƙin ciki sosai a kan Shawulu. Ubangiji kuwa ya damu da ya sa Shawulu ya zama Sarkin Isra’ila ba.


Kuma Ishaya ya ce, “Tushen Yesse zai tsiro, wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai; al’ummai za su sa bege a gare shi.”


Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala.


Sai Sama’ila ya ɗauki ’yar kwalabar mai, ya zuba man ɗin wa Shawulu a kansa, ya yi masa sumba yana cewa, “Ubangiji ya keɓe ka shugaba bisa gādonsa.


Amma Sama’ila ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba. Ka ƙi maganar Ubangiji, Ubangiji kuma ya ƙi ka da zama sarki a bisa Isra’ila.”


“Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga ƙasar Benyamin. Ka keɓe shi shugaban mutanena Isra’ila. Shi zai cece mutanena daga hannun Filistiyawa. Na ga azabar mutanena gama kukansu ya hauro wurina.”


“Na damu da na naɗa Shawulu sarki, domin ya juya mini baya, bai kuma bi umarnina ba.” Sama’ila ya damu ƙwarai, ya yi kuka ga Ubangiji dukan dare.


Ana ce da su azurfar da aka ƙi, gama Ubangiji ya ƙi su.”


Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida. Sa’an nan annabin ya zuba wa Yehu mai a kā, ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na naɗa ka sarki a bisa jama’ar Ubangiji, wato, Isra’ila.


Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.


“Saboda haka kada ka yi addu’a don wannan mutane ko ka yi wani kuka ko roƙo dominsu, gama ba zan ji ka ba.


Duba, na mai da shi shaida ga mutane, shugaba da kuma jagorar mutane.


A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja.


Sa’an nan ka ɗauki kwalabar man ka zuba a kansa, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, na naɗa ka sarkin Isra’ila.’ Sa’an nan ka buɗe ƙofa ka ruga a guje; kada ka ɓata lokaci!”


Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi!


“Kada ka yi addu’a domin wannan mutane ko ka miƙa wani roƙo ko kuka dominsu, domin ba zan saurara ba sa’ad da suka kira gare ni a lokacin ƙuncinsu.


Toho zai fito daga kututturen Yesse; daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.


Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa,


‘Tun ran da na fitar da mutanena Isra’ila daga Masar, ban zaɓi wani birni a cikin wata kabilar Isra’ila a gina haikali domin Sunana yă kasance a can ba, amma na zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’


Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, suka yi yarjejjeniya da shi a gaban Ubangiji, suka kuwa shafe Dawuda ya zama sarki a bisa Isra’ila, yadda Ubangiji ya yi alkawari ta wurin Sama’ila.


“Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila.


Sai ya ce, “Waɗannan su ne biyun da aka shafe don su yi wa Ubangiji dukan duniya hidima.”


To, Dawuda dai ɗan wani mutumin Efratawa ne mai suna Yesse, shi mutumin Betlehem ne a cikin Yahudiya. Yesse yana da yara maza takwas, a zamanin Shawulu kuwa, Yesse ya riga ya tsufa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ