Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Samaʼila 14:12 - Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Mutanen da suke sansanin suka kira Yonatan da mai ɗaukan makamansa da babbar murya suka ce, “Ku hauro wajenmu, mu kuwa za mu koya muku hankali.” Sai Yonatan ya ce wa mai ɗaukan makamansa, “Biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra’ila.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

12 Sai suka kira Jonatan da mai ɗaukar makamansa, suka ce, “Ku hauro zuwa wurinmu, mu faɗa muku wani abu.” Jonatan kuwa ya ce wa mai ɗaukar makamansa, “Ka biyo ni, gama Ubangiji ya bashe su a hannun Isra'ilawa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Samaʼila 14:12
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da zarar ka ji tafiya kamar na takawar sojoji tana a bisan itatuwan balsam, sai ka yi maza, gama wannan alama ce cewa Ubangiji ya sha gabanka don yă karkashe sojojin Filistiyawa.”


Sai Amaziya ya aika ’yan aika wurin Yehowash ɗan Yehoyahaz, ɗan Yehu, sarkin Isra’ila, yana tsokanarsa cewa, “Zo, mu sadu fuska da fuska.”


Amma in suka ce mana, ‘Ku haura wurinmu,’ to, sai mu haura, wannan zai zama mana alama cewa Ubangiji ya bashe su a hannunmu.”


Da Gideyon ya ji mafarkin da fassararsa, sai ya yi wa Allah sujada. Ya koma sansanin Isra’ila ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Ku tashi! Ubangiji ya ba da sansanin Midiyawa a hannuwanku.”


Sa’an nan Debora ta ce wa Barak, “Je ka! Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da Sisera a hannunka. Ba Ubangiji ya riga ya sha gabanka?” Saboda haka Barak ya gangara zuwa Dutsen Tabor, da mutum dubu goma biye da shi.


na kuma sunkuya na yi wa Ubangiji sujada. Na yabi Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim wanda ya bi da ni a hanyar da take daidai, don in samo wa ɗan maigidana jikanyar ɗan’uwansa.


“Sa’ad da na zo rijiya a yau, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ina roƙonka ka ba ni nasara a tafiyar da na yi.


Da sauri ya kira mai riƙon masa makami ya ce, “Zaro takobinka ka kashe ni, don kada a ce ‘Mace ce ta kashe shi.’ ” Saboda haka bawansa ya soke shi, ya mutu.


Sai Yonatan ya hau dutsen da rarrafe, mai ɗaukan makamansa kuwa yana biye. Yonatan ya yi ta fyaɗa Filistiyawa da ƙasa, mai ɗaukan makamansa kuma ya yi ta karkashe su.


Abokinsa ya ce, “Ai wannan ba wani abu ba ne fiye da takobin Gideyon ɗan Yowash, mutumin Isra’ila. Allah ya ba da Midiyawa da dukan sansani a hannuwansa.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ