Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 8:7 - Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka sa’ad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

7 Amma dai ba kowa ne yake da wannan sani ba. Amma waɗansu ta wurin sabawarsu da al'amuran gunki har yanzu, sukan ci naman da suka ɗauka kamar an yanka wa gunki ne. Saboda haka lamirinsu, da yake rarrauna ne, ya ƙazantu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 8:7
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne.


A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.


Ni kaina na tabbata, ’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi.


To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina.


To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.”


Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito,


Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ