Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.
Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.
Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa.
Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.
Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.
Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki.