1 Korintiyawa 6:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Ba ku san cewa tsarkaka ne za su yi wa duniya shari’a ba? In kuwa za ku yi wa duniya shari’a, ai, kun isa ku yi shari’a a kan ƙananan damuwoyi ke nan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Ashe, ba ku sani ba, tsarkaka ne za su yi wa duniya shari'a? In kuwa ku ne za ku yi wa duniya shari'a, ashe, ba za ku iya shari'ar ƙananan al'amura ba? အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.