Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu lambu kuma ya sa iri ya yi girma, haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo su tsiro a gaban dukan al’ummai.
domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku.
Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata
Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.
Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.
Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai.
Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”