To, fa ’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba.
Ba ta wurin doka ce Ibrahim da zuriyarsa suka sami alkawarin cewa zai zama magājin duniya ba, amma sai dai ta wurin adalcin da yake zuwa ta wurin bangaskiya.
cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.