Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.
Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana.
Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.