Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Korintiyawa 2:9 - Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

9 Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa, “Abubuwan da ido bai taɓa gani ba, Kunne bai taɓa ji ba, Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba, Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Korintiyawa 2:9
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji, babu kunnen da ya gane, babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai, wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.


Alherinka da girma yake, wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka, wanda ka mayar a gaban mutane a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.


Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.


Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa.


Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba?


“Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.


A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau, ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.


“Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.


Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.


Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.


Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ